13 Yuni 2023 - 20:09
Gwamnatin Ali Khalifa Ta Kame Wasu Matasa 'Yan Shi'a Uku 'Yan Bahrain

Gwamnatin Ali Khalifa Naci Gaba Da Kama Matasa 'Yan Shi'a 'Yan Bahrain

 Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, tashar Rasad kuma mai bin diddigin hare-haren da aka kai a kasar Bahrain cewa: Sojojin gwamnatin al-Khalifa a ranar Juma'a 9 ga watan Yunin 2023 sun kama "Yusuf Ghalib" daga mutanen yankin Aali a wani hari da suka kai a Karzakan.

A yammacin ranar Asabar ne dakarun gwamnatin Al-Khalifa suka mika dan Sheikh Hassan Ali Razi "Muhammad" zuwa wani katafaren gini na binciken manyan laifuka kafin daga bisani a mayar da shi gidan yarin Al-Hawz Al-Jaf inda Ofishin mai gabatar da kara ya bayar da umarnin a tsare shi na tsawon kwanaki bakwai domin amsa tambayoyi.